Duk lokacin da za mu yi bal, kafin a take wasa ina cika baki da cewa sai na ci. Sai mutane su yi ta mamaki idan naci ɗin. To ba wani abu ba ne illa Expected Goals (xGs).
xGs yana gaya ma yadda zaka ci ƙwallo: daga wajen da ya kamata ka tsaya, daga ina ya kamata ka buga, har zuwa irin bugun da za ka yi, da sauran su.
Duk da yawancin ƙwallon da muke ƴar manɗo ce, idan ka duba a babbar bal ma haka abin yake, tun da daga can ne na aro wannan dabara.
Wanda suka san ƙwallo, ko da kuwa basu san fasahar xGs ba da wannan sunan, sun san cewa akwai ɓangaren da indai ka buga bal to zai wahala ba ka ci ba.
Masana xGs a ilimance kan iya bada bayanin ƙungiyar da za tai nasara tun kafin a take wasa. Shi yasa lokacin wasan ƙarshe na Kofin Duniya na cewa Habibu Ɗan’Ana kar ya damu, lokacin da ya ce ba zai je kallon wasan ba. Yana ganin kamar da matsala, amma nace masa kar ya damu, Spain ne za su ci. Ba don komai ba, xGs na nuna cewa su ne za su ci.
Idan za ku iya tunawa, akwai wani lokaci da Manchester United lokacin Sir Alex Ferguson suka ci kofina har uku a lokaci guda: Kofin Zakarun Nahiyar Turai, Kofin Premier League da na FA duk a watan Mayun 1999. Wane mutum! Lokacin shigowar fasahar xGs ke nan ba daɗewa, kuma Sir Alex na daga cikin masu horarwa na farko-farko da suka karɓe ta. Abin yana sabo, tun kafin a waye. Haka dai, Liverpool suka zo, su ka yi tashen su, kafin Manchester City su karɓi ludayin.
Idan za ku iya tunawa ma a 2018 Liverpool sun je wasan ƙarshe na Gasar Zakarun Nahiyar Turai, duk da an cinye su, kuma suka sake dawowa suka ci gasar a shekarar 2019-2020. Suka ƙara zuwa wasan ƙarshe a shekarar 2022. A shekarar 2020 kuma, Liverpool ɗin dai sun ci gasar Premier League, bayan shafe shekara 30 ba tare da sun ci gasar ba. Kofinan da suka ɗauka a ɗan tsakanin sun haɗa da kofin Club World Cup, European Super Cup, FA da kuma League Cups guda biyu. Wannan duk saboda Jürgen Klopp ya rungumi fasahar xGs ne.
Ƴan caca ma suna amfani da xG kafin kaɗa ludo gabanin wasa.
To menene xGs (Expected Goals)?
xGs wata hanya ce da ake amfani da na’ura mai ƙwaƙwalwa don lissafa yiwuwar cin bal a wasa. Abubuwan da ake dubawa kusan guda 6 sun haɗa da: 1) tazarar bugu (shot) daga bakin raga, 2) ɓangaren da akai bugu, 3) wane irin bugu aka yi, 4) yanayin ƴan baya da matsin lambar da suka sa akan ɗan wasa, 5) sai kuma irin taimako (assist) da ɗan wasa ya samu da kuma na ƙarshe, 6) wato yanayin samun bal, a cikin rububi aka samu ko kuma gaba da gaba akai da ɗan-baya (1v1).
A matakin farko ke nan.
Idan muka motsa sama kaɗan, xGs na amfani da wasu muhimman bayanai guda biyu, abinda ake kira da “event data” da kuma “location data” a lokacin wasa. Ana amfani da waɗannan bayanan ne don samun duk abin da ake buƙata don gano wa zai yi nasara a wasa, ta hanyar naɗar duk wani abu da ya faru a yayin wasa. Zan tsaya haka, don bazan shiga da nisa ba kan wannan bayanin.
Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da dama sunƙi rungumar hikimar xGs lokacin da ta shigo. Sun nuna tirjiya da suka, amma bayan wani lokaci, sai aka zo aka rungumeta hannu bibiyu. Yau ta kai-ta-kawo babu wata ƙungiyar ƙwallo me amsa sunanta a duniya da ba ta amfani da wannan fasaha, musamman a Yammacin duniya.
Yanzu shi ne idan ka duba bayan rabun lokacin duk wani wasa da kuma ƙarshen sa, za ka ga abin da ake cewa "statistics", wato ƙididdigar abin da ya faru a wasa. Kai me kallo iya abin da ka ke iya gani ke nan, iya saninka. Amma ƙwararru suna da bayanan da ya wuce haka. Ta haka ake gane ƙungiyar da tafi ƙoƙari ko da kuwa idanunka ba su nuna maka hakan ba.
xGs zai ba ka bayanin duk abin da yake faruwa, ko ya faru a wasa, kama daga yawan taɓa ƙwallo har i zuwa ɓangaren da ya fi cin bal.
Daga bayanan “location data” da aka gina na tsawon lokaci, ƙididdiga ta nuna cewa ba a fiya cin bal daga tazara me nisa daga raga ba. Ga masu Kallon bal, musamman Premier League, an san cewa abubuwa sun canja. Yanzu an daina cin ƙwallo daga tsakiyar fili kamar yadda aka saba lokacin su Scholes, Lampard, Gerrard da Ballack.
Ga masu taka leda da kuma yin video game tun daga SEGA har zuwa PS series da Xbox, za ka gane cewa akwai ɓangaren da indai ka shigo bakin raga ka buga to zai wahala baka ci ba. To wannan abin ba haka nan ya ke ba, da dalili.
Abin da ka ke gani ba komai ba ne illa xGs, domin kuwa abin da yake faruwa a zahiri aka kwafo a ka ɗora a na’ura. Shin ma wai, ka taɓa tambayar kanka ta yaya ƴan-wasan video game suke kusan kama da na gasken, da ɗabi’unsu da komai? Musamman wajen cigaban da aka samu na baya-bayannan a FIFA Series kamar wajen bugu (shot), gudu, tsaro? Ka taɓa tambayar kanka yadda hakan ta kasance, kaga Haaland kamar Haaland ɗin? xGs, domin kuwa tana bibiyar duk abin da yake faruwa a yayin wasa sannan ta adana waɗannan bayanan don amfanin gaba.
Mu koma baya, ko nace mu ɗora daga inda muka tsaya. Idan kana ganin cewa kamar abin da nake faɗa ba-wai, cewa akwai inda indai ka buga bal sai ka ci, to akwai wurare ma ko yanayin motsi a cikin fili da indai ka yi to ba wanda zai kama ka. Masana ƙwallo da kyau sun san abin da ake cewa “passing lanes”. Hanyoyi ne da ake zira bal da ba wanda ya isa ya kama. Ƴan wasan Barcelona ko duk wani ɗan wasa da Pep Guardiola ya horar, to zaka ga sun fi kowa sanin wannan. Arteta na Arsenal shi ma gwani ne a wanna fannin. Kamar titin jirgi ne da ake fa ɗa, sai kaji kamar almara wai titi a sama. Duk wanda yake hawa jirgi yasan haka abin yake. Idan kai mazaunin Kurna ne to ka san cewa jirgi yana wucewa ta unguwarku. Me yasa? Amsar ɗaya ce. To haka abin yake a filin bal. Ita ma bal tana da titinta a filin ƙwallo kuma indai an ɗora ta to da ƙyar a kama. Wannan shi ake cewa “diagonal passing in a passing lane”. xGs ce zata nuna ma haka idan iliminka ya kai. Kuma ana koyawa ƴan-wasa yadda ake yin sa.
Akwai ma ƙarin wani salon gudu da ake yi akan titin yayin wasa. Indai ka kama layi ka fita, tofa sai Allah. Ana ce masa diagonal run, ni kuma in ace masa gudun Messi, yanzu kuma gudun Lamine Yamal. Daga wannan gudun ake shiga kusurwar shaiɗan, wajen haɗari ke nan. Indai ka kai-kaito, kamar yadda Garzali yake faɗa, to sai kuɗin. Domin kana bugawa to ci ne kawai. Wanda yafi kowa cin irin wannan bal ɗin a yanzu shi ne Kylian Mbappé.
Sanin wannan yasa indai na zo fili kafin a take wasa nake cika baki.
Ba wai nafi kowa iya ƙwallo ba ne, sai dai kawai sanin yadda harkar ta ke.
Ni ban ma san da waɗannan littattafan ba tun asali. Tun tsawon lokaci kawai na gane cewa akwai wani salo da ake yiwa leda, Allah kuwa. Duk wanda yake video game zai iya sanin haka. Kwatsam kuma, ina cikin bincike da karance-karance, sai na ci karo da fasahar xGs. Na ce ehhhh, ashe?! Ina ƙara bincike kawai sai naga ashe ma bayan maƙaloli da aka wallafa har llittattafai ma an buga.
Ya kamata kai ma daga yau ka ringa zuwa kana duba xGs kafin kowanne wasa. Sannan ka sake komawa ka duba sakamakon wasa bayan an tashi don tabbatar da sahihancin xGs. Yawanci abinda xGs ta faɗa shi yake tabbata, duk da ba kullum ake kwana a gado ba, kamar wasan Arsenal da Liverpool makon da ya gabata.



No comments:
Post a Comment