Garin mu ƙarmi ne, yana kusa da Chicago. Kamar Jigawa da Kano. Duk lokacin da naje Najeriya, idan na dawo, jirgi ya sauke ni a Chicago, sai na hau mota na kama hanyar garinmu.
A cikin kusan shekeru ukun farko da nayi a nan, ban taɓa zuwa wata jaha ba, face wata rana da muka je Iowa ni da wasu abokaina, Turawa, muka yi kwana biyu. Ko cikin garin Chicago ban taɓa shiga ba.
Wata rana sai taro ya zo a Chicago. Duk da bani da gami da taron kai tsaye, sai aka ban baki, na shirya na je, ganin cewa akwai mutane daga Najeriya da suka zo, ƴan uwa da abokan arziƙi da ya kamata a gaisa.
Ina shiga Chicago daga nan na gane ashe a ƙauye nake. Ai ni yau ne na fara zuwa Amerika. Ashe duk sallamar da nake yiwa mutane a Najeriya nace na tafi Amerika ba Amerika nake zuwa ba, ƙauye nake zuwa.
Jama’a garin mu fa ya haɗu, kawai dai ƙarami ne. Hada-hada da hayaniyar jama’a ba kamar Chicago ba. Abin da aka fi sanin garinmu da shi ita ce Jami’a. Ga aminci, ba hayaniya. Akwai garuruwa da dama a Amerika masu irin wannan suffar da ake kira da College Town, wato garuruwan da makaranta ce ginshiƙinsu. Har wata ran cewa nake yi wanna shiru yayi yawa.
A kaf ƙasar Amerika, garinmu na ɗaya daga cikin na gaba-gaba a kyawun zama saboda rashin tsadar sa da kuma tarbiyya. Yana ɗaya daga cikin garuruwa na farko don matasa auren fari kuma marasa ƙarfi, don gina kansu da iyalansu (the best place for the young and broke and the best place to raise the family). Hukumomin birnin na shirya bita duk shekara wa matasan da suka zo karatu garin don ƙarfafa musu gwiwa kan su zauna bayan kammala karatunsu.
Garin ƴan makaranta ne, kamar yadda na ce, irin Dutse ko Zaria. Idan lokcain hutu ya yi, ya kan zama shiru idan ɗalibai sun tafi. Akwai tarbiyya. Har ta kai da a aji muna iya gane ɗalibai ƴan asalin garin saboda kamalarsu.
Ina ƙaunar garin, don haka kar kayi mamaki idan ka ji na ce “garinmu”. Rayuwa tana da inganci, ga sauƙi, duk da muna na ashirin a ƙarfin tattalin arziƙi a baki ɗayan ƙasar. Jami’ar garin ita ce ginshiƙin tattalin arziƙin garin. Har ana cewa idan ka tara mutum goma, to takwas daga ciki na da alaƙa ta kusa ko ta nesa da ita.
***
Kwatsam sai ga tafiya zuwa New York ta zo, wadda awa biyu ce a jirgin sama, kwana ɗaya ko biyu a mota, ya danganta da jadawalin motar da ka samu.
Tsawon shekaru ana ta ce min ya kamata na kai ziyara wasu garuruwan, na ɗan zagaya naga gari, naga yadda Amerika take. Akwai abin da yasa mutane suke faɗar hakan, bawai kawai don yawon buɗe ido ba. Duk da dai ba su bayyana a fili ba, masu wannan batu na jin tsoron halin da ake ciki, kar lokacin gama karatuna ya yi ba ne jo ko’ina ba, na kasa samun aiki, kuma na koma gida. Domin shugaban ƙasa Donald Trump ya kunnawa baƙi wuta.
Ni kam sai dai na ce to, na ƙyale, don ni zama a garin Amerika ba ɗa-ɗa ni ya yi da ƙasa ba. Na ɗauke shi rabi-da-rabi ne. Idan na zauna toh, idan ban sami aiki na zauna ba, sammakal.
Matsain lambar Trump yasa wasu ɗaliban ƴan ƙasar waje basa iya zuwa gida hutu. Ni kam ba abin da ya shallan. Sai ka ji an ce, cikin mamaki da fargaba, musamman ƴan Najeriya ƴan Kudu, “Za ka je Najeria”?!. Na ce ehh, nai murmushi. To, ni na kasa ganewa. Amerikan garinmu ce? Ina zuwa gida duk ƙarshen zangon karatu ba tare da la’akari da haɗarin da hakan ke tattare da shi ba.
Muna yara, idan almajiran makarantar allonmu za su je gida Nijar, sai muyi ta mamaki. Ikon Allah, ga ruwa, ga wuta, ga titi ga komai, amma su a haka duk za su bar wannan su tafi? Me su ka rasa a nan da za su tafi gida? Sai yanzu na fahimta.
A matsayina na malami, duk ƙarshen zangon karatu ɗalibai kan tambayeni cikin hira ko awkai shirin wani abu da na ke da shi idan muka gama ajujuwa? Sai su cika da mamaki idan na ce zan je Najeriya.
Da Kofin Duniya ya zo, kuma za a yi wasan ƙarshe a New York/New Jersey (za ka ga ana rubuta New York-New Jersey, su ɗin kamar Makoɗa ne da Ɗanbatta). Don haka sai naje na sayi tikitin tafiya. Na duba na ga farashin tikitin jirgi da na mota. Mota tafi jirgi tsada. Da akwai ban-bancin wajen dala hamsun a tsakanin su. Amma sai dai shi jirgi kamar Spirit da Frontier ba za ka hau da kaya ba, sai dai jakar goyo kawai.
Ni kam ina da kaya, kuma akwai saƙo da zan baiwa wanda zan je wajen sa. Turawa kam su sun saba. Sukan iya hawa jirgin abin su. Idan suka yi lissafi sai su ga sauƙin hakan, don za ka iya samun canji da kuɗin jirgin har ka sayi kayan sawar da ka ke so idan ka sauka.
Na isa tashar mota minti talatin kafin tafiya. Da isata na kama waje na zauna, ina jiran mota ta zo. Motoci na ta zuwa, su sauke fasinja su sa ke lodi. Da naga lokacin da ya ke jikin tikitin motata yana ƙaratowa, sai naje na samu direban wata mota da take lodi na tambayeshi “Ko yaushe wannan motar zata zo”? Na nuna masa tikitina, na faɗi sunan kamfanin. Yace nan ba da jimawa ba.
Can sai ga wata budruwa ƴar tsatson Somalia.
Tace min “mota ta tafi ko, Flexi Bus?”
Na ce kai ba tabbas.
“Ina za ki je ne?”.
Ta ce min “Miami”.
Na ce kai ba lallai ta tafi ba. Ni ban ga Flexi Bus ta zo ba.
Wannan ce tafiyata ta farko zuwa wani garin da ba Chicago ba a motar haya. Amma na san duk motocin da suke zuwa wannan tashar. Ina wucewa ta wajen sosai. Idan hanya ta haɗa akan gansu suna lodi a wajen.
Bayan mintina sai matashiyar ta tafi.
Tafiyarta ke da wuya, baifi kamar minti shida ba, sai ga motar Flexi Bus ta zo. Kowa ya nuna tikiti ya shiga. Mota ta yi lodi ta tafi. Can sai ga wata motar ta sake zuwa, ita ma tayi lodi ta tafi. Da naga lokaci ya na ta tafiya, har ya wuce lokacin da ya kamata ace motar mu ta zo da kamar minti biyar, sai na ce to ai me yiwuwa ana sami tsaiko a hanya ne, sakamakon cunkoso ko aikin titi da ake ta yi (saboda yanzu lokacin bazara ne, lokacin yin aikin titina ne kafin sanyi da ƙanƙara su dawo).
Can dai, da naga abin ya yi yawa, har mun shiga latti na kusan minti talatin, sai na kira lambar wayar kamfanin don naji ina a ka kwana. Wata mata ta ɗau waya. Na fara yi mata jawabin abin da yake faruwa. Ta ce na karanto mata bayanai na da na sayi tikiti da su: suna, lambar tikiti da imel. Na fara da suna, Abubakar: A as in Apple, B for ball, U for uniform…R for ring… har i zuwa ƙarshe. Indai za kai waya da kamfani ko ofishin gwamnati, to haka za ka faɗi sunanka don gudun kuskure, shi ne hanyar da za su fi ganewa. Tun abin yana ban haushi har ya koma bani dariya. Idan kuma kai tsaye ne naje ofishi, to da na je bakin kanta sai na miƙa adanti kati ɗina.
Mata tace ce ai mota ta zo a dai-dai lokacin da aka bata kuma ta tafi. Nace sam, banganta.
Mata fa ta dage. Ni ma fa na dage. Ta dage na dage, ana ta tirka-tirka. Da naga ba fa haza, sai na ce to yanzu meye abin yi? Ina mafita? Yanzu ya za ai da ni?
Ta ce to ko dai na jira na hau motar ƙarfe 7:30 dare, ko kuma na kai kaina birnin Chicago inda motar da na rasa zata yada zango. Idan na riske ta a can sai na hau na tafi.
Nan fa na fara tunani, na tsaya ko na tafi ko na koma gida? – amma kawai sai na sayi tikiti zuwa Chicago na kamfanin wata motar, mu ka kama hanya muka tafi, da kamar karfe biyu da kwata na rana. Damuwar, ba yadda za ai mu iya wuce motar. Indai mutum ya wuce ka a titi, indai ba tare kuke tafiya ba, to zai wahala ka kamo shi ko ma ka wuce shi, indai ba wata matsala ya samu ba. Dailili kuwa shi ne, a tsarin sufuri a nan, duk wanda ya riga ka barci sai ya riga ka tashi. Har dai za ka bi ƙa’idar tuƙi, akwai adadin gudu da za ka yi, kuma sai ka bi umarnin fitilar titi, da suaransu, to zai wahala ka wuce wanda yake gabanka.
Muka kama hanya muna tafiya, mu tsaya mu sauke fasinja mu ɗauki wasu, har mu ka kusa isa Chicago. A ƙa’ida kamar tafiyar awa uku ce, zamu isa cikin gari kamar 6:30 na yamma, har lokacin da muka ɓata kafin mu fito bakin gari mu hau hanya. Mun kama hanya mun yi nisa, sai direba yace to fa baa za mu iya isa ba sai 7:30, saboda yamma ce, mutane sun tashi daga aiki suna ƙoƙarin komawa gida akwai cinkuso. Jiki na ya yi sanyi, amma dai ban karaya ba.
Ni dai kamar na yi tsun-tsu, kamar na koma gida, kamar kawai na sayi tikitin jirgin sama na hau daga Chicago.Na rasa me zanyi. Na yi ta da-na-sani, ina waswasi.
Tun a baya abin da ya hana ni komawa gida shi ne kar abokai na su ganni kuma na tafi na dawo. Ga shi an sha wahala, sai naga tun da har an yanka kazar to ya kamata a fige.
Haka na zauna a cikin mota ina ta tunani. Ba mu isa Chicago ba sai ƙarfe 7 da motsi. A wannan lokacin mota tuni ta tashi. Na rasa me zan yi.
Sai na tambayi direba, Baƙin Ba-Amerike da ya kawo mu, na ce “Don Allah ina ne inda tashar motar Greyhound ta ke?”, kamfanin motar da zan hua ke nan. Sune suke harkar sufuri da jigilar fasinjan gari-gari a Amerika da Canada.
Direba ya kwatanta min, yace idan na bi nan sai nai can, idan na wuce gini huɗu, sai nayi hagu. Tafiyar minti takwas ce a allon map da na duba. Na kama hanya, kamar fa na ɓace. Ga shi ina kallo a wayata, ina gani mintuna kaɗan ne, amma na kasa zuwa. Sai shatale-tale na ke a banza. Sai na fara tare mutane ina tambaya. Wasu su tsaya, wasu kuma su wuce abin su ko kula ni ba sui ba. A zaton su ko zan roƙe su kuɗi ne domin an fi samun mabarata a cikin Baƙeƙen fata, wanda cikin su ne talauci ya fi yawa. Wasu su tsaya su ji batuna, amma sai su ce basu san wajen ba. Da ƙyar na samu wani wanda ya sake ɗora ni a hanya.
Da isa cikin tashar, sai na ga motoci birjik, suna ta shiga suna fita. Fasunjoji na shiga mota, wasu kuma na fita. Idan mota ta sauke fasinja ta huta, sai a sake mata lodi ta fita. Sai na ga har da Flexi Bus, motar da ta zo garinmu. Nai salati na sanar da Ubangiji. Kuka zan yi ko dariya?
Sai na ce tohh haka a ka yi!
Sufurin mota kamar na jirgi ya ke – haɗin gwiwa – ka sayi tikitin wannan mota, wata kuma ta ɗauke ka ta kai ka wani wajen, wata ma ta sake ɗaukar ka, har ka je inda za ka je. Ba mota ɗaya ce za ta kai-ka ba kai-tsaye Gwammaja Ƴan-Kura.
Ashe ma kamfanin Greyhound da Flexi Bus abu ɗaya ne. Flexi Bus ne suka siye kamfanin Greyhound suka haɗe. Amma ba su canja masa suna ba saboda shi a ka fi sani.
Sai naje kan kanta wajen wata mata, Ɓaƙar Amerika me ɗan-jiki. Nayi mata bayani abin da ya faru. Da alama sun saba ganin irin haka. Ta ce maza, kira wannan lambar, ta nuna wata lamba a manne a jikin bango. Na kira, nai mata bayani. Cikin sa’a, matar da na yi magana da ita ɗazu ita na sake riska.
Ina fara karanto bayanai na kawai na ji ta gane. Bayan wasu mintina, sai ta ce na duba imel ɗina. Nan take na duba. Sai ga tikiti ya shigo, nace mata e na ga tikiti, na ƙara da cewa amma an soke shi tare da jadawalin tsohuwar tafiyar. Tace na sake dubawa, bayan shi akwai wani. Na sake dubawa. Sai ga shi an canja min tikiti, an sani a motar da za ta tashi ƙarfe 11:30 na dare, cikin awanni uku da rabi masu zuwa. Ita wannan mota ita ce dai za ta ɗauke ni da ace na tsaya a garinmu na biyo motar 7:30 ɗin.
Ilai, sai ga shi an kashe tsaohon tikiti an bani sabo, an kuma cire kuɗin zuwa Chicago da ban hau ba an dawo min da su. Ni fa har na cire rai, don na san yadda za ai ta kai ruwa rana a Najeriya.
Duk wanda ya ke harkar sufurin ƙasa-da-ƙasa ta jirgin sama to zai sha mamaki a tafiyarsa ta farko yadda harkar jirgi ta ke, musamman ta jigilar mutane da kayan su. Za a tattaro mutane daga garuruwa daban-daban, gaba ɗayan ku za a cireku daga wannan jirgi, a saka ku a wani, a haɗe a gwamutsa, amma kaya ba sa ɓata, sannan kuma ba a kuskuren siyar da tikitin da ya fi yawan kujerun jirgi.
Za ku sayi tikiti watanni daban-daban, daga ƙasashe daban-daban kafin tafiya, amma haka za a tattaro na Kano da na Beijin, da na Berlin da na Cape Town a kai su Qatar, sannan a zuba su a jrigi ɗaya dai zai kai su New York. Kuma kowa zai zo a jirgi daban da jakunkunan su daban-daban.
Muka hau mota da misalin ƙarfe 11:30 na dare mu ka kama hanya. Mu sauka nan, mu tashi can, har mu ka isa garin Detroit na Jihar Michigan da misalin ƙarfe 5 na safe. Nan ne muka yada zango, inda kowa ya sauka don can ja mota zuwa inda kowa zai je. Haka dai, motoci sai shigowa suke yi cikin tasha, wasu su sauke fasinja wasu su ɗauka. Motar mu za ta tashi da misalin ƙarfe 11 na safe, wanda daga nan kuma sai tasha ta gaba, Pennsylvania. Amma a hanya mun shiga ta Ohio, inda muka kwashi wasu fasinjoji a garuruwa daban-daban na Ohion, kamar su Toledo da Cleveland, sai dai a irin waɗannan garuruwa ba a tsayawa mai-yawa don canja mota. Sai dai a tsaya na ƴan mintina fasinja su hau ko su sauka. Wani wajen kuma a bada minti kamar biyar, wanda zai siyo abinci ya saiyo, wanda za iyi fitsari ya yi.
***
Pittsburgh, Pennsylvania
Tafiyar duka dai kwana biyu ce, mu tsaya a nan mu yada zango, mu yi gaba mu ƙara lodi. Mun shiga garuruwa da dama, a ƙalla guda 7, daga ciki har da Illinoi, Indiana, Michigan, Ohio, sai Pennsylvania, sai kuma New Jersey sannan ita kanta New York.
A duk cikin garuruwan da muka je ba wanda ya fi burge ni kamar Pittsburgh, Pennsylvania. Ba wai don garin yafi sauran garuruwan Amerika ba, a’a, sai dai kawai cewa yanayin zubin ƙasar garin ya ban-banta da sauran.
Duk manyan biranen Amerika na da manyan benaye da hanyoyi, suna da wuta da ruwa marasa yankewa, suna da wuraren shaƙatawa da more rayuwa da kuma wuraren al’adu da tarihi. Ko’ina da irin abubuwan da suke da shi, da kuma gudunmawar da suke bayarwa.
Yanayin zubin Pittsburgh ba irin ragowar garuruwa ba ne. Pittsburgh na da yanayi mai wuyar sha’ani. Garin na da tudu da kwari, yanayin hawa da gangare, ramuka, tsaunuka da kwazazzabai masu maban-bantan tsayi da zurfi, sai kuma duwatsu, dazuzzuka da bishiyu malale a ko’ina.
A wani wajen tsaunukan sun miƙa sama ƙoƙoluwa, har su kan kama daga ƙafa 1,500 zuwa 3, 000 da motsi. Sai kuma wani yankin da yake da kwazazzabai, da ramuka masu zurfin gaske da ruwa a ciki. Wani yankin nada rafuka, koguna da kwazazzabai masu zurfi.
A nan a ke yin ta! Duk abin da ka ke ji ba nanata zance ba ne. Duk akwai waɗannan maban-bantan yanayi a garin.
Ina ƙoƙarin kawo maka yadda abun yake ne a zahiri; duk da hakan nada sarƙaƙiya, musamman ganin cewa akwai ban-bancin yadda muke kallon ilimi da kuma yadda Bature yake kallon sa. Tangarɗar shi ne cewa saƙon a gaskiya ba zai fita yadda ya kamata ba. Amma ba damuwa za mu yi ba, saboda hakan zai kai mu kai tsaye inda nake so mu je. Domin fahimtar me nake nufi, ka je ka rubuta ‘Pennsylvania topography’ a yanar gizo, za ka ga abin da zai fito, kuma ka mayar da hankali bisa abin da zai biyo baya a rubutunnan nan gaba kaɗan.
Fahimtar garin Pittsburgh kamar yadda yake haƙiƙa na buƙatar yare na musamman, a nan muna iya cewa kan fannin ƙasa da muhalli tunda shi muke magana akai, wanda ban sani ba a Hausa idan akwai. Bisa wannan dalili, abubuwa da dama ba za su fito fili ba yadda ya kamata, wanda hakan tawaya ce. Ga misali, ya za a faɗi waɗannan a Hausa: landslide, earthquake, slope failure, ground collapse?
Kusan duk abu ɗaya ne, amma kowanne akwai dalilin da yasa a ka bashi suna daban. Don haka ba ɗaya ba ne. Dole ne yadda za a faɗe su ya kasance ya bayyana abin da suke yi ko yadda suke ko aikin da yake faruwa a zahiri. Ba ta fuskar rahoto ba da za a hakaito abin da yake faruwa, a’a, ta fuskar samar da ilimi, ko bayanin da zai iya ceton rayuka ko halakar da su, asarar dukiya ko akasin haka, ko kuma samar da sabuwar hanyar bunƙasa harkokin yau da kullum.
Lura da wannan bayani, ga misali, kana mai ƙudurce cewa kuskure ɗaya, duk ƙanƙantarsa zai jawo – ba wai zai iya jawowa ba – a’a kai tsaye zai jawo gagarumar matsala, zai hana yin abin da a ke so a yi gaba ɗaya, kamar gina gari irin Pittsburgh mai wuyar sha’ani:
“Wealthy cities in hazardous sites such as Los Angeles or Tokyo can reduce geological or meteorological risk through massive public works and “hard engineering”:” stabilizing landslides with geotextiles nets, gunnite, and rock bolts; terracing and regrading oversteep hillsides; drilling deep drainage wells and pumping water out of saturated soils; intercepting debris flows with small dams and basins; and channeling storm runoff into vast systems of concrete channels and sewers”.
(Planet of Slums, 124)
Ƴan magana suka ce: tunaninka kamannunka.
Aiki sai mai shi.
Irin wannan ilimi da fahimtar ire-iren mabanbantan yanayi da zubin ƙasa na garin Pittsburgh shi ya bada damar gina garin, kuma a ka iya yiwa garin yadda ake so. Wani wajen an yiwa ƙasar hikima, wani wajen an yi mata dole, wani wajen kuma an hau tabarmar sulhu.
Shi dai wannan gari, a kowanne lokaci a duk inda ka ke, za ka iya kasancewa a saman tsauni da ya kai ƙafa 3,000; ko kuma cikin kwazazzabo da ya kai ƙafa 1,500 ko 2,000. Ga kuma ruwa da ya zo ya keta garin ta ko’ina, kamar River Ohio, wanda ba ɗaya ba ne ba biyu ba. Hakan ya sa garin ko ina gada ce, wata ta keta can, wata ta keta nan, wasu a tare gungu-gungu, wasu kan wasu, kuma ba wai na ado ba ne irin na Chicago don samar da hanyoyin mota. A’a, wannan gadoji na dole ne, dan samar da hanyoyin sufuri da zirga-zirga. Wasu gadojin sun tsallaka saman ruwa, wasu kuma saman kwazazzabai. Wani kwazazzabon zurfinsa ya kai ƙafa 2, 000 ko 3,000, idan ka faɗa ko kukan ka ba za a ji ba, amma haka a ka shiga a ka saka harsashin gada a ciki.
Da adadin gadoji 446, ana yiwa garin Pittsburgh take da Garin Gadoji (City of Bridges), kuma kimanin mutane milyan 2.3 ne kacal a garin idan ka kwatanta da Kano. Babaan abin mamaki shi ne yadda a ka sarrafa zubin ƙasar dan gina garin da samar da abubuwan zamantakewa na dole da za su tallafi rayuwa.
Saman tsauni ka ga gida, gefen sa kwazazzabo. Wani tsaunin kuma ya kai tsauni ba zai yiwu a keta shi ai titi ba, sai akai haƙa ta cikin sa a ka yi ramin titi ya yuce (tunnel). A saman irin wannan tsauni kuma sai ka ga an share wata ƴar hanya inda layin wuta ya bi ta kai ya wuce. Ko kaga eriya sabis akai.
Abu dai iri-iri, ya danganta da yadda wajen ya zo da kuma me ake so a yi. Wani wajen ya yi makaifa, wani wajen ya yi kwanciyar magirbi, wani wajen ya yi rami a makaifa, wani wajen tsauni ne ya yi sama kuma mai kwanciyar magirbi, wani wajen kwazzabo ne ya kai-kaita, amma duk da haka ba a fasa yin abin da a ke so ba.
Ni dai ina zaune cikin mota ina ganin ikon Allah. Ruwa, tsauni, rafi da dazuzzuka sun ratsa garin ta ko’ina.
Lokacin da Turawa su ka zo, sun tarar da ƴan gargajiya ba sa iya zuwa inda su ke so ta daɗin rai. Su kan su Turawa lokacin sai sun haura ruwa ko sun hau dutse kafin mutum ya je inda ya ke so. Don haka Turawa su ka fara gina gadojin itace kafin daga bisani su maye su da na ƙarfe. Amma fa wannan ana maganar shekara 208 da ta wuce ne, daga 1818 zuwa yau, 2026, lokacin da aka fara gina gadojin katakon bayan an sha gwagwarmawa kafin fahimtar muhallin da kuma ƙirƙiro kayan aikin gini da kimiyyar su.
Sababbun zuwa muka ciro waya muna yin hoto. Ina ganin wasu Indiyawa suna ankarar da juna abubuwan mamakin da suke gani. Sai juye-juye suke suna ɗaukar hoto. A zuciya ta na ce “colonized people”, yadda aka yiwa Sarakunan Arewa da wasu masu iko a Afrika ke nan lokacin mulkin mallaka. Sai a ɗauki Sarakuna da ƴan jarida irin su Abubakar Imam a kai su London, sai su dawo cikin mamaki da jin-jinawa Bature. Hakan ya zama wata waƙi’a da take tabbatar da mulkin Turawa akan Baƙaƙe, tunda dai su Turawa har gobe sun yarda cewa, a faɗin su, “It is unnatural to be ruled by your inferior”. Kuma dai, game da Baƙaƙe, suka sa ke cewa, “If you are not inferior, you will not be one second dominated”. Idan kuma ka yi musu, Turawa suka ce, to me ya sa kai a ka yi wa mulkin mallaka ba kai ka yi ba, me ya sa kai a ka mamaya ba ka kai ka mamaya ba, me ya sa kai a ke juyawa a halin yanzu ba kai ka ke juyawa ba?
Wannan zai sa ke haska maka me yasa Iraniyawa su ka zaɓi su mutu a kan su bari Turawa su danne su. A wannan tunanin dai, za ka fahimci cewa duk wata matsala da ka ke ciki ka na ciki ne saboda gazawar ka, saboda matsalar tafi ƙarfin ka, amma ba wai don matsalar ba ta da magani ba ne ko ta gagara.
Tunaninka, kamanninka.
Labarin kai manyan Arewa London ya tuna min da abin da Turawan mulkin mallakar dai su ka yi a Gabashin Africa, musamman Tanganyika, Tanzania a yau. Sai su ɗau Baƙaƙe su kai su bakin Ruwan Victoria. Sai su nunawa Baƙi gadar da suka gina, wadda ita ce ta farko a Afrika da ta tsallaka ruwa ta haɗa garuruwan gefe. Ƴan Afrika su kalla su girgiza kai, wane mutum, su kuwa Turawa su ce: “engineering wonder”. Hakan ya nunawa ƴan Afrika cewa ehh, dole a mulke ku. Kuma dama al’ƙawarin Allah ne cewa ilimi shi ke mulkar jahilci.
Da muna hira da wani Baƙar fata kan abin da na gani a Pittsburgh, sai ya ce to na je Sin? Domin shi ya je, kuma abin da ya gani ba wasa ba. Sin ta wauce hankali. Ai Amerika ba komai ba ce, a faɗar sa. Na ce na yadda, amma dai lokacin da Amerikawa su ka yi wannan aiki fa babu ilimin kimiyya da fasaha da hikimar gine-gine da tsara birane irin na yanzu. Babu inda za ka siyo mashina da kayan aiki ko ka kwafo. Duk abin da za ka yi, sai dai ka ƙir-ƙire shi da kanka, inji ne ko mashin. Shi kansa mashin ɗin da ya ke yin mashin sai dai ka yi shi.
Ni dai a raina cewa na yi da a ce mutanen mu ne su ka je Amerika, to da wani wajen cewa za a yi ban da shi, musamman wajen su Pittsburgh da ke da wuyar sha’ani. Don wani wajen sai an fasa dutse, kuma dutse ba na wasa ba. Wani wajen sai kayi tafiyar mintina a cikin rami, wani wajen kuma gada ce gaba siyaki baya damisa, sai dai ka ga kana lilo kamar a siraɗi.
Baya ga titina, an gina gidaje a saman tsaunuka da kwazazzabai an kai musu ruwa da wuta, ba maganar tudu ko kwari ko fargabar ambaliyar ruwa ko girgizar ƙasa. Allah kawai Ya san ilimin da a ka gano kuma a kai amfani da shi wajen gina garin Pittsburgh.
Can mu ka tsallaka wani ruwa, muka shiga asalin garin Pittsburhg, inda zuciyar garin ta ke, inda a ke hada-hada. Abubuwan da za ka fara karo da su su ne samaniyar garin, cike da dogayen benaye masu nunawa sama yatsa. Adadin dogayen benayen garin ya kai 115, wanda 34 daga ciki sun wuce tsawon ƙafa 300. Sannan ƙasan garin a rarake yake, kamar ragowar garuruwa, inda nan ne layin dogo yake, da kwatoci da layin ruwa, da sauran su, daga ƙasa ta ɗaya har zuwa abun da ya sawwaƙa.
Yanzu damina ce a Nejeriya, na ga mutane sai ƙorafi suke ruwa na cika musu layi.
Pittsburgh na da tasiri a ƙasar Amerika. Garin ya samar da manyan ƴan kasuwa kuma hamshaƙai, irin su Andrew Carnegie da Andrew Mellon, waɗanda sune su ka kafa cibiyoyi da gidauniya iri-iri, wanda su ke ɗaukar nauyin bincike kala-kala, kamar na kimiyya da fasaha da sha’anin zamantakewar ɗan-Adam, ƙungiyoyin sa-kai, harkokin mulki da gwamnati da sauran su.
A cikin wasu cibiyoyin bincike da kowannensu ya kafa, Andrew Carnegie mai Carnegie Technical Schools, da kuma Andrew Mellon mai Mellon Institute of Industrial Research, cibiyoyin na su guda biyu sai suka haɗe a shekarar 1967 suka zama Carnegie Mellon University. Don haka a fannin ilimi garin Pittsburgh ba baya ba.
Bayan da Andrew Carnegie da takwaransa Andrew Mellon suka gama tara dukiya, sai su ka ba da waqafin wani kaso daga cikin dukiyarsu ga harkokin bincike da faɗaɗa ilimi. Duk da su attajirai ne da su kai shuhura a cinikayyar ƙarfe da gawayi da gina layin dogo da hada-hadar kuɗi da bankuna, ba abin da ya fi taimakon su wajen tara musu dukiya illa ilimi da bincike. Ilimi ne ya basu damar gano sabbin hanyoyin sarrafa abubuwa kuma suka kere sa’a. Don haka su kai masa tagomashi.
Idan ka je unguwar Oakland, inda a nan Jami’ar Carnegie Mellon ta ke, tare da Jami’ar Pittsburgh, babban abin da zai ɗau hankalinka shi ne Music Hall da Library. Gine-gine ne na alfarma zubin Rumawa. Da yake Pennsylvania na ɗaya daga cikin garuruwa 13 da Turawa su ka fara dira, har yanzu akwai irin tsofaffin gidajen da suka haura shekara 200 da mutane ke zuwa don ganin tarihi da yawon buɗe ido.
Idan mu ka dawo gida Kano, wannan ya sa dole a jinjinaya Mallam Isyaku Rabiu da ahalinsa, da irin su Alhassan Ɗantata da ire-iren su. Ba yadda za ai ka zo Kano baka ga tasirin su ba. Tasirunsu ya ɗanfaru a garin Kano, daga gine-ginen gidajensu, makarantu har i zuwa masallatai.
Kamar su Andrew Carnegie da Andrew Mellon, su ma haka su ke a Kano, duk da mun so su fi haka.
Muna fatan samun irin su da yawa.
Ƙarshe.